Iran Ta Yi Allawadai Da Matakin Buritaniya na Haramta Kungiyar Hezbollah
(last modified Sat, 02 Mar 2019 13:07:18 GMT )
Mar 02, 2019 13:07 UTC
  • Iran Ta Yi Allawadai Da Matakin Buritaniya na Haramta Kungiyar Hezbollah

Jamhuriya Musulinci ta Iran, ta yi allawadai da matakin mahukuntan birnin Londan, na haramtawa da kuma sanya kungiyar Hezbollah, ta kasar Lebanon, cikin jerin kungiyoyin 'yan ta'adda.

Da yake sanar da hakan, ministan harkokin wajen kasar ta Iran, Muhammad Jawad Zarif, ya ce matakin na Buritaniya, abun takaici ne, kana kuma ba zai taimnaka ba wajen samar da tsaro da kwanciyar hankali a kasar ta Labanon ba.

A ranar Litini data gabata ne ministan harkokin cikin gida na Burtaniya, Sajid Javid, ya zargi kungiyar ta Hebollah da ci gaba da dagula al'amura da kuma halin da ake ciki a yankin gabas ta tsakiya.

Burtaniya dai ta ce babu bambanci a wajenta tsakanin bangaren kungiyar Hebollah mai dauke da makamai da kuma na siyasa, wanda takai ga sanya suna kungiyar cikin jerin 'yan ta'adda, da kuma tanadin zaman gidan yari na tsawan shekara goma ga duk wani dan kasar da yayi hulda da kungiyar.

Matakin da tuni kasashen Amurka da Isra'ila, sukayi marhabin dashi.