Pars Today
Jamhuriya Musulinci ta Iran, ta yi allawadai da matakin mahukuntan birnin Londan, na haramtawa da kuma sanya kungiyar Hezbollah, ta kasar Lebanon, cikin jerin kungiyoyin 'yan ta'adda.
Mahukuntan Moscow da Landon sun dawo da huldar diflomatsiya tattaunawa a tsakaninsu bayan shafe watanni 11, tun bayan kiki-kakar da ya shiga tsakaninsu kan batun jami'an leken asirin nan na Rasha Skripal.
Firai Ministan kasar Britania Thereser May ta isa birnin Brussels na kasar Belguim dangane da shirin ficewar kasarta daga tarayyar Turai.
Wasu majiyoyin labarai a kasar Siriya sun bayyana cewa sojojin kasar Britania 5 ne suka halaka a lokacinda yan ta'adda na kungiyar Daesh wadanda har yanzun suke iko da yankin Dair-Zur daga gabacin kasar suka cilla makamai masu linzami a kansu.
Jami'i mai kula da harkokin tsaro a Maikatar harkokin cikin gidan Birtaniya Ben Wallace ya ce; Kungiyar alka'ida tana da niyyar kai wasu sabbin hare-hare akan filaye jiragen sama a nahiyar turai
Bangarorin dake rikici a Yemen, sun sanar da amince wa da shirin tattaunawa na Majalisar Dinkin Duniya domin samar da zaman lafiya a kasar.
Biritaniya ta gabatar wa kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya, da wani daftarin kudiri kan dakatar da bude wuta da yadda za a samu kai kayan agaji ga al'ummar kasar Yemen.
Ministan harkokin wajen Biritaniya, Jeremy Hunt, ya gana da takwaransa na Iran Mohammad Jawad Zarif, a birnin Tehran a yau Litini.
Dubban mutanen kasar Britania sun fito zanga zanga a birnin Londan ta kasar Britania inda suke bukatar gwamnatin kasar ta dakatar da shirin ficewa daga tarayyar turai, wanda ake kira Brexit.
Manzon musamman na kasar Birtaniya kan bunkasa harkokin kasuwanci tsakanin kasar da kuma Iran Lord Norman Lamont, ya bayyana hukuncin kotun duniya kan karar da Iran ta shigar kan Amurka da cewa yana da muhimmanci.