Ministan Harkokin Wajen Biritaniya Na Ziyara A Tehran
(last modified Mon, 19 Nov 2018 15:14:25 GMT )
Nov 19, 2018 15:14 UTC
  • Ministan Harkokin Wajen Biritaniya Na Ziyara A Tehran

Ministan harkokin wajen Biritaniya, Jeremy Hunt, ya gana da takwaransa na Iran Mohammad Jawad Zarif, a birnin Tehran a yau Litini.

A yayin ziyarar bangarorin biyu sun tattauna kan batutuwan da suka shafi kasar Yemen, makomar yarjejeniyar nukiliyar da aka cimma da Iran.

A game da halin da halin da ake a Yemen, Mista Hunt, ya ce lalle lalle suna da matukar ganin an samu zaman lafiya a Yemen, sannan a game da batun yarjejeniyar nukiliyar Iran kuwa Ministan harkokin wajen Biritaniyar ya nanata goyan bayan mahukuntan Landan na ci gaba da mutunta yarjejeniyar.

Wannan dai iat ce ziyarar farko ta wani ministan harkokin wajen Biritaniya a Iran tun bayan da Amurka ta janye daga yarjejeniyar da manyan kasashen duniya suka cimma da Iran a shekara 2015.