Nov 19, 2018 16:44 UTC
  • Masu Rikici A Yemen Sun Amince Shiga Shirin Samar Da Zaman Lafiya

Bangarorin dake rikici a Yemen, sun sanar da amince wa da shirin tattaunawa na Majalisar Dinkin Duniya domin samar da zaman lafiya a kasar.

Wata sanarwa da bangaren gwamnatin kasar mai murabus dake samun goyan bayan Saudiyya ta fitar a yau, ta ce a shirye take ta shiga tattaunawar da ake shirin yi karkashin jagorancin MDD a Swiden.

Wannan dai na zuwa ne bayan da bangaren 'yan gwagwarmaya na Houthi ya sanar da cewa, a shirye yake ya dakatar da bude wuta idan har bangaren da ke yaki da su na kawancen da Saudiyya ke jagoranta ya tsagaita bude wuta.

Dama dai kafin hakan kawancen da Saudiyya ke jagoranta ya bada umarnin dakatar da bude wuta a garin na Hodeida da ke gabar teku.

A wani labari nan daban kasra Biritaniya ta gabatar wa kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya, da wani daftarin kudiri a yau kan dakatar da bude wuta da yadda za a samu kai kayan agaji ga al'ummar kasar Yemen.

Kawo yanzu ba'a dai sanar da ranar da za'a kada kuri'a kan daftarin kudirin ba.

Tags