Oct 07, 2018 07:15 UTC
  • Lord Norman: Hukuncin Kotun Duniya Kan Karar Da Iran Ta Shigar Yana Da Muhimmanci

Manzon musamman na kasar Birtaniya kan bunkasa harkokin kasuwanci tsakanin kasar da kuma Iran Lord Norman Lamont, ya bayyana hukuncin kotun duniya kan karar da Iran ta shigar kan Amurka da cewa yana da muhimmanci.

A lokacin da yake zantawa da kamfanin dillancin labaran IRNA a jiya Asabar, Lord Norman Lamont ya bayyana cewa ko shakka babu hukuncin na kotun duniya abu ne mai matukar muhimmanci, musamman ma ga kasar Iran.

Ya ce duk da cewa takunkumin Amurka ba zai hana yin mu'amala tsakanin kasarsa da Iran ba, amma matakin da alkalan kotun suka dauka na bin kadun wannan batu, tare da tabbatar da halascin yin mu'amala tare da Iran bisa doka, lamari ne mai karfafa gwiwa.

A ranar Laraba da ta gabata ce a zaman da kotun duniya da ke birnin Hague ta gudanar, ta tabbatar da rashin halascin takunkumin Amurka a kan kasar Iran.

Tags