Marassa Karfi Na Samun Taimako Daga Musulmi A Birtaniya
(last modified Sat, 03 Jun 2017 20:21:30 GMT )
Jun 03, 2017 20:21 UTC
  • Marassa Karfi Na Samun Taimako Daga Musulmi A Birtaniya

Mabiya addinin muslunci a birnin Northamptonchron na kasar Birtaniya suna taimaka ma sauran jama’a marassa karfi a cikin wannan wata.

Yusuf Miya shugaban kngiyar bayar da agaji ta musulmi a wannan birnin yana cewa, yana daga cikin kyawawan ayyuka na wannan wata taimaka ma marassa karfi.

Ya ce addinin muslunci ya koyar da musulmi kyawawan dabiu da suka hada da tausaya wad an adama, ba tare da yin la’akari da addininsa ko akidarsa ba, kuma babbar hikimar azumin watan Ramadan ita ce tarbiyantar da musulmi a kan tausayi da taimakon maras shi.

An fara gudanar da wannan shiri ne daga jiya kuma zai ci gaba har zuwa karshen watan azumin watan Ramadan mai alfarma, inda za a rika bayar da abinci a lokacin buda baki ga musulmi da ma wadanda ba musulmi.

Musulmin birnin Northamptonchron suna gudanar da irin wannan ayyuka a kowace shekara, kamar yadda a wasu biranan ma na kasar Birtaniya, ana gudanar da ayyuka na jin kai da taimakon marassa karfi a irin wannan lokaci da ake gudanar da ibadar azumin watan mai alfarma.