Pars Today
A yayin da aka kwashe shekara guda ana gudanar da zanga-zangar neman dawo da hakkin kasa a yankin Palastinu, Hukumar kare hakin bil-adama ta MDD ta ce akwai bukatar Isra'ila ta gudanar da sauye-sauye a jerin dokokin jami'an tsaronta.
Piraministan kasar Faransa, Edouard Philippe, ya sanar da korar shugaban 'yan sanda birnin Paris, biyo bayan mummunar zanga zangar da masu bore a kasar da aka fi sani da masu dorawa riga, sukayi a ranar Asabar data gabata.
Kungiyar kare hakkin bil adama ta kasa da kasa Amnesty International ta bukaci a kame tare da hukunta dukkanin shugabannin kungiyoyi masu nuna kyama ga musulmi a duniya.
Dangin mutumin da ya kashe musulmi a kasae New Zealand sun nemi gafarar musulmi da kuma sauran al’ummar kasar, dangane da abin da Brenton Tarrant ya aikata.
A Indonusiya adadin mutanen da suka ras arayukansu a ambaliyar ruwa ya kai 58, a cewar hukumar kula da agajin gaggawa ta kasar.
Rahotanni daga Faransa na cewa zanga zangar da masu dorawar riga keyi, na ci gaba da kamari, inda a jiya Asabar masu boren suka kona shaguna tare da kwasar ganima a babban titin ''Champs-Elysées'', na Paris babban birnin kasar.
Sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pempeo ne ya sanar da cewa; kasarsa za ta ci gaba da kakaba wa Iran din takunkumi, kuma Washington tana son ganin an daina sayen man fetur din Iran kwata-kwata.
Kungiyar kare hakkin bil adama ta kasa da kasa Amnesty International ta bayar da kakkausan martani dangane da harin da aka kaiwa musulmi a kasar New Zealand.
Kasa da sa'oi ashirin da hudu da kai harin kasar New Zealanda kan musulmi, an kai wani harin a kan wani musulmi a birnin London na kasar Birtaniya.
Saktare janar na MDD cikin wani bayani da ya fitar ya yi allah wadai kan harin ta'addancin da aka kaiwa musulmi a kasar New zeland sannan ya ce ya zama wajibi a hada kai wajen yakar masu kyamar musulmi a Duniya