Mar 17, 2019 16:25 UTC
  • Indonusiya : Mutum 58 Suka Mutu A Ambaliyar Ruwa

A Indonusiya adadin mutanen da suka ras arayukansu a ambaliyar ruwa ya kai 58, a cewar hukumar kula da agajin gaggawa ta kasar.

Hukumar ta ce akwai yiyuwar adadin mutanen ma ya karu, kasancewar jami'an agaji har yanzu suna kokarin kaiwa ga yankin da lamarin ya faru domin gudanar da ayyukan ceto.

kakakin hukumar Sutopo Purwo Nugroho, jami'ai na kokarin isa yankunan da lamarin ya faru saidia suka fuskantar tsaiko saboda rashin kyawan hanyoyi da bishiyoyi suka toshe da kuma cabo.

Bayanai sun nuna cewa akwai gidaje da dama da suka lalace.

A ranar Asabar data gabata ne aka fuskanci ambaliyar ruwa a yankin Sentani biyo bayan sabkar ruwa tamakar da bakin kwarya da aka fuskanta a yankin.

Tags