Indonusiya : Mutum 59 Suka Mutu A Ambaliyar Ruwa Da Zaftarewar Kasa
(last modified Fri, 25 Jan 2019 05:11:06 GMT )
Jan 25, 2019 05:11 UTC
  • Indonusiya : Mutum 59 Suka Mutu A Ambaliyar Ruwa Da Zaftarewar Kasa

A Indonusiya adadin mutanen da suka rasa rayukansu a iftila'in ambaliyar ruwa da zaftarewar kasa ya kai 59.

Tunda farko dai an bayyana cewa mutum talatin ne suka rasa rayukansu a lamarin, saidai alkalumman baya baya nan da hukumar agajin gaggawa ta kasar ta fitar ta ce adadin ya linka zuwa 59.

Haka zalika akwai yiyuwar adadin ya karu, kasancewar akwai wasu mutane 25 da suka bata.

Kimanin mutane 3,400 ne aka ceto bayan ruwan sama tamakar da bakin kwarya da aka shashara hade da iska mai karfin gaske a kudancin tsibirin (Célèbes) dake tsakiyar kasar da ya haddasa tambatsewar magudannan ruwa a yankin.

Bayanai sun nuna cewa gomman kyauyuka ne suka fuskanci ambaliyar ruwa, a cikin larduna 12 na yankin da kuma wani yanki na tsibirin.

Matsalar kuma ta fi yin barna a lardin Gowa, inda aka samu gawarwakin mutane 44.

Zaftarewar kasa da kuma ambaliyar ruwa, sun shahara a Indonusiya, musamman a lokutan damuna, inda ko a watan Oktoba da ya gabata mutane 20 suka mutu a cikin irin wannan yanayi a tsibirin Sumatra dake yammacin kasar.