Dec 23, 2018 10:36 UTC
  • Indonusiya : Mutum 168 Suka Mutu A Ambaliyar Tsunami

Rahotanni daga Indonisiya na cewa mutum 168 ne suka rasa rayukansu, kana wasu daruruwa suka jikkata, biyo bayan aman wutar tsauni data haddasa ambaliyar tsunami.

A sanarwar da hukumomin kasar suka fitar a yau, sun kuma ce ambaliyar ruwan tayi awan gaba da gidaje masu yawa.

Alkalumman da mahukuntan aksar suka fitar sun ce mutum 168 suka mutu, wasu 745 sun raunana sai kuma 30 da suka bata, kuma akwai yiyuwar alkalumman su karu.

Hukumar bada agajin gaggawa ta kasar, ta ce aman wutar da wuni dutse ya yi ne ya haddasa ambaliyar ta tsunami, wadda ta afkawa yankunan Kudancin Sumatra da Java da misalin karfe 9 na daren jiya agogon kasar ba tare da an Ankara ba.

Indonesiya dai ta fi kowace kasa fuskantar hatsarin aukuwar girgizar kasa, aman wuta daga tsaunuka da kuma ambaliya a wasu lokutan, kasancewar ta a yankin Pacific, wadda daga karkashinsa aka fi samun yawaitar motsawar kasa.

 

Tags