Amurka Na Ci Gaba Da Kakaba Wa Al’ummar Takunkumi
Sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pempeo ne ya sanar da cewa; kasarsa za ta ci gaba da kakaba wa Iran din takunkumi, kuma Washington tana son ganin an daina sayen man fetur din Iran kwata-kwata.
Sakataren na harkokin wajen Amurka ya bayyana haka ne a jiya Asabar a yayin da yake gabatar da wani jawabi a birnin Houston na jahar Texas a Amurka
A ranar 8 ga watan Mayu na shekarar da ta gabata ne dai shugaban kasar Amurka Donald Trump ya sanar da ficewar kasarsa daga yarjejeniyar Nukiliya da Iran.
Amurkan ta sake dawo da takunkuman da ta kakabawa Iran gabanin cimma yarjejeniyar ta 2015.
Sai dai sauran kasashen da suka hada Rasha, China, Birtaniya, Faransa, da Jamus, sun azamar ci gaba da aiki da yarjejeniyar.