-
Kungiyar Amnesty Int. Ta Yi Kakkausar Suka Kan Cin Zarafin 'Yan Adam Myanmar
Feb 24, 2017 09:05Kungiyar kare hakkin bil adama ta Amnesty Int. ta yi Allawadai da kakakusar murya dangane da kisan kiyashin da aka yi wa musulmi a Myanmar.
-
Isra'ila, Al-Sa'ud Da Al-Khalifa: Tushen Laiffuffukan Yaki Da Take Hakkokin Bil'adama
Feb 24, 2017 01:20Laifin yaki na daga cikin muhimman laifuffukan da aka yi bayanin ma'anarsa a fili ciki takardu da dokokin kotunan kasa da kasa. Sashi na 8 na dokokin hukunta laifuffukan na kasa da kasa yayi bayanin abubuwan da suke tabbatar da laifin yaki, wanda daga cikinsu akwai kisan gilla, azabtarwa mai tsanani, cutar da jikin mutum, kai hari da gangan kan fararen hula, ruwan bama-bamai kan gidajen mutane ko gine-ginen da ba na soji ba da kuma amfani da makamai masu guba da iskar gas mai makure mutum.
-
Magance rikicin Siriya ba ya bukatar shigar Soja
Feb 24, 2017 00:58Manzon MDD kan rikicin Sirya Steffan de Mistura ya ce kowa ya san cewa magance rikicin kasar Siriya ba ya bukatar shigar Soja.
-
Babban Sakataren M.D.D Ya Gabatar Da Shawarar Samar Da Ofishin Sanya Ido Kan Ayyukan Ta'addanci
Feb 23, 2017 14:17Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya ya gabatar da shawarar samar da wani ofishi a Majalisar da zai dinga sanya ido tare da gabatar da rahoto kan irin ayyukan ta'addancin da ke faruwa a duniya.
-
An yi alawadai da harin ta'addancin da aka kai kasar Iraki
Feb 23, 2017 07:24Kwamitin tsaro na MDD ya yi alawadai kan harin ta'addancin da aka kai kasar Iraki
-
Samar Da Kasashe 2 Ne, Zai Magance Rikicin Palestinu Da Isra'ila, Inji Hollande
Feb 23, 2017 02:13Shugaba Francois Hollande, na kasar Faransa, ya bayyana cewa samar da kasashe biyu ita ce kawai mafita wajen magance rikicin Palestinu da Isra'ila.
-
Za'a Je Zagaye Na Biyu A Zaben Equador
Feb 23, 2017 02:13Majalisar zabe a Equador, ta ce za'a je zagaye na biyu a zaben shugaban kasar, bayan da aka kasa samun wanda ya samu adadin kuri'un da ake bukata domin lashe zaben tun zagayen farko.
-
Sabon Zagayen Tattaunawar Geneva Kan Rikicin Syria
Feb 23, 2017 02:12A yau Alhamis ne, wakilan gwamnati da 'yan adawa na Syria ke sabon zamen tattaunawa a Geneva, da nufin samar da zamen lafiya a wannan kasa da rikicin shekaru shida ya daidaita.
-
Wata Kotun Afirka Ta Kudu Ta Hana Gwamnatin Kasar Ficewar Daga Kotun ICC
Feb 22, 2017 14:26Wata kotu a kasar Afirka ta Kudu ta fitar da hukuncin dakatar da gwamnatin kasar daga yunkurinta na ficewa daga kotun kasa da kasa mai hukunta manyan laifuka wato ICC.
-
Damuwar Kungiyar kare hakin bil-adama kan yadda ake cin zarafin Al'umma a kasashen Afirka
Feb 22, 2017 07:31Kungiyar kare hakin bil-adama ta bayyana damuwar ta kan yadda ake amfani da karfi wajen cin zarafin Al'umma a Nahiyar Afirka.