Magance rikicin Siriya ba ya bukatar shigar Soja
https://parstoday.ir/ha/news/world-i17970-magance_rikicin_siriya_ba_ya_bukatar_shigar_soja
Manzon MDD kan rikicin Sirya Steffan de Mistura ya ce kowa ya san cewa magance rikicin kasar Siriya ba ya bukatar shigar Soja.
(last modified 2018-08-22T11:29:43+00:00 )
Feb 24, 2017 04:28 UTC
  • Magance rikicin Siriya ba ya bukatar shigar Soja

Manzon MDD kan rikicin Sirya Steffan de Mistura ya ce kowa ya san cewa magance rikicin kasar Siriya ba ya bukatar shigar Soja.

Tashar telbijin din Al'alam dake watsa shirye-shiryenta daga nan birnin Tehran ta nakalto Manzon MDD kan rikicin Sirya Steffan de Mistura a yayin bude taron Ganeva na 4 na cewa domin magance rikicin kasar Siriya MDD na bukatar goyon bayan mahalarta taron.

De Mistura ya kara da cewa Kwamitin tsaron MDD ya kira dukkanin bangarorin dake rikci da juna da su halarci taron ba tare da sun gindaya wani sharadi ba,wanda hakan zai taimaka wajen samun maslaha da kuma mafuta na warware rikicin. to saidai Manzon MDD ya sanya shakku kan cimma matsaya a wannan zama sanadiyar tsauraran sharrudan 'yan tawaye.

A daren jiya Alkhamis ne aka buda taron Gavrva na 4 a kasar Suizilland, inda wakilin kasar Siriya a MDD Bashar Ja'afari ya jagoranci tawagar Gwamnati, a yayin da Nasr Hariri ya jagoranci tawagar 'yan tawaye.

Tun daga shekarar 2011 ne aka fara rikicin kasar ta Siriya bayan da wasu kasashen Larabawa bisa jagorancin masarautar Ali-sa'oud tare da goyon bayan kasar Amurka suka dinga kwaso matasa daga kasashen Duniya tare da basu horon ta'addanci suna kuma tura su cikin kasar ta Siriya domin kifar da halarcecciyar Gwamnati ta Bashar Al-asad.