MDD:An Fara Gudanar Da Taron Geneva Karo Na Takwas
Kakakin majalisar dinkin duniya ya sanar da fara taron Geneva karo na takwas domin magance rikicin kasar Siriya.
Kamfanin dillancin lrna ya nakalto kakakin MDD Stephane Dujarric na cewa tun a marecen jiya Talata tawagar 'yan adawar siriyan ta gana da Staffan de Mistura wakilin MDD kan kasar Siriya kuma ana sa ran a yau Laraba tawagar gwamnatin Siriya za ta gana da de Mistura.
A ranar 14 ga watan Yunin da ya gabata ne aka kawo karshen tattaunawar Geneva ta 7, wannan tattauna na zuwa ne a yayin da kasashen Iran, Rasha da Turkiya suka gabatar da shawarar magance rikicin na Siriya ta hanyar kiran taron 'yan kasa da zai hada dukkanin 'yan siysa,da wakilan kabilun kasar ba tare da katsalandan na kasashen waje ba.
A ranar Larabar da ta gabata ce dakta Hasan Rauhani da Viladimin Putin na kasar Rasha tare da Rajab Tayyib Erdogan na kasar Turkiya suka tattauna a birnin Sochi na kasar Rasha domin neman mafuta na magance rikicin kasar siriya.
A karshen taron shugabanin kasashen sun gabatar da taron manema larabai, inda suka tabbatar da cewa manufa da kuma sakamakon taron, kafa wani kwamiti da zai gudanar da babbar taron 'yan kasar Siriya da ya hada dukkani wakilan kabilu, wakilan mazhabobi da na 'yan siyasa domin magance matsalar kasar su.