Sabon Zagayen Tattaunawar Geneva Kan Rikicin Syria
A yau Alhamis ne, wakilan gwamnati da 'yan adawa na Syria ke sabon zamen tattaunawa a Geneva, da nufin samar da zamen lafiya a wannan kasa da rikicin shekaru shida ya daidaita.
Ana dai bayyana wannan sabon zagayen tattaunawa da mai cike da tsarkakiya, bayan zagaye ukun da akayi a cen baya ba tare da shawo kan rikicin kasar ba.
Mai shiga tsakani na MDD kan rikicin kasar ta Syria, Satafan de Mistura ya bayyanawa manema labarai shakkunsa akan ko tattaunawar zata haifar da da mai ido.
A wani mataki na karfafawa tattaunawar Kasar Rasha dake da fada aji a rikicin ta bukaci kawarta Syria data dakatar da kai hare-haren sama a duk lokacin tsawan wannan tattaunawar ta hudu a Geneva.
A baya bayan dai 'yan adawa sun sha korafi akan abunda suka kira ci gaba da keta yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cimma da gwamnati keyi saboda hare-haren da take kaiwa a kusa da biranen Damas da kuma wasu kauyukan Homs a tsakiyar kasar.