-
MDD Ta Nuna Damuwarta Kan Ci Gaba Da Tsare Wani Alkalinta Da Ake Yi A Turkey
Nov 10, 2016 02:23Majalisar Dinkin Duniya ta nuna damuwarta dangane da ci gaba da tsare wani alkalin da majalisar ta nada don yin shari'ar kisan kiyashin da aka yi a Yugoslavia da Rwanda da gwamnatin Turkiyya ta yi bisa zargin hannu cikin kokarin juyin mulkin da ya faru a kasar.
-
'Yan Sandan Spain Sun Tarwatsa 'Yan Kungiyar Masu Shigar Da Matasa Kungiyar ISIS A Kasar
Nov 10, 2016 02:23Ma'aikatar harkokin cikin gidan kasar Spain ta sanar da cewa 'yan sandan kasar sun sami nasarar tarwatsa 'yan wata kungiyar 'yan ta'adda da suke kokarin janyo hankula kananan yara da matasa da shigar da su cikin kungiyar ta'addancin nan ta Da'esh (ISIS) a kasar.
-
Ministocin harkokin Wajen Turai Za Su Gudanar Da Taro Na Musamman Kan Nasarar Trump
Nov 10, 2016 02:22Sakamakon ci gaba da fargabar da kasashen duniya suke nunawa kan nasarar da Donald Trump ya samu a zaben shugabancin Amurka, Ma'aikatar harkokin wajen kasar Jamus ta sanar da cewa ministocin harkokin wajen kasashen Kungiyar Tarayyar Turai za su gudanar da wani taro na musamman don tattaunawa kan nasarar da Trump din ya samu.
-
Rasha za ta fara kai farmaki kan 'yan ta'adda a Siriya
Nov 09, 2016 07:52Wata majiya a Ma'aikatar tsaron Rasha ta ce nan ba da jimawa ba Dakarun tsaron kasar za su fara kai farmaki kan 'yan ta'adda a garin Alepo
-
Zaman Taron Kasashen Da Suke Makobtaka Da Libiya A Birnin Adis Ababa Na Kasar Habasha
Nov 09, 2016 02:20Shugabannin kasashen da suke makobtaka da Libiya da kuma mambobin kwamiti na musamman da kungiyar tarayyar Afrika ta kafa kan yin nazari dangane da halin kasar ta Libiya ke ciki, sun fara gudanar da wani zama na musamman domin tattauna halin kasar.
-
Donald Trump Na Kan Gaba A Zaben Amurka
Nov 09, 2016 02:19Rahotanni daga Amurka na cewa dan takarar jam'iyyar adawa ta Republican Donald Trump, ke kan gaba a sakamakon zaben shugaban kasa da aka kada kuri'arsa a jiya Talata.
-
َAna Ci Gaba Da Kada Kuri'u Na Zaben Shugaban Kasa A Kasar Amurka
Nov 08, 2016 13:04Tun daga sanyin safiyar yau ne miliyoyin masu zabe a kasar Amurka suka fara kada kuri'unsu a zaben shugaban kasa a jihohi 50 na fadin kasar
-
Zaben Shugaban Kasa A Amurka
Nov 08, 2016 04:34A yau ne mutanen kasar Amurka za su gudanar da zaben shugaban kasa karo na 45 a kasar, wanda zai maye gurbin Barack Obama.
-
Wasu Masu Kyamar Musulunci Sun Kai Hari Kan Masallaci A Sweden
Nov 08, 2016 04:31Wasu masu tsananin kyamar musulunci sun kai hari kan wani masallaci a unguwar Ringby da ke cikin birnin Stockholm fadar mulkin kasar Sweden.
-
Shugaba Asad: Kasashen Yammaci Na Ci Gaba Da Rauni A Kasar Siriya
Nov 06, 2016 14:05Shugaban kasar Siriya, Basshar al-Asad ya bayyana cewar manyan kasashen yammaci na ci gaba da yin rauni a yakin da ke gudana a kasarsa alhali kuwa dakarun gwamnati da suke samun goyon bayan dakarun sa kai na al'ummar kasar suna ci gaba da samun nasarori kan 'yan ta'addan da aka shigo da su kasar daga kasashe daban-daban na duniya.