Donald Trump Na Kan Gaba A Zaben Amurka
Rahotanni daga Amurka na cewa dan takarar jam'iyyar adawa ta Republican Donald Trump, ke kan gaba a sakamakon zaben shugaban kasa da aka kada kuri'arsa a jiya Talata.
Wannan dai na nuna Donald Trump ya kama hanyar lashe zaben na Amurka a fafatawar da yayi da 'yar takara demokrat Hillary Clinton da ke samun goyon bayan shugaba mai barin gado Barack Obama.
Ana dai bukatar dan takara ya samu wakilai 270 daga cikin 538 domin samun nasara, inda yanzu Donald Trump keda wakilai sama da 250, yayin da Cliton keda 215.
Har ila yau bayanai na nuna cewa jam'iyyar Republican ce keda rinjaye a majalisar wakilan kasar, bayan da dan takara ya lashe wasu muhimman jihohi.
ko baya ga hakan bayanai daga kasar sun nuna cewa kasuwannin hannayen jari sun fadi tun bayan da alamu suka fara nuna cewa Misis Clinton na fuskantar koma baya.
Wannan zaben dai shi na aka bayyana a matsayin wanda yafi raba kanuwan al'ummar Amurka.