Wasu Masu Kyamar Musulunci Sun Kai Hari Kan Masallaci A Sweden
https://parstoday.ir/ha/news/world-i13549-wasu_masu_kyamar_musulunci_sun_kai_hari_kan_masallaci_a_sweden
Wasu masu tsananin kyamar musulunci sun kai hari kan wani masallaci a unguwar Ringby da ke cikin birnin Stockholm fadar mulkin kasar Sweden.
(last modified 2018-08-22T06:59:12+00:00 )
Nov 08, 2016 04:31 UTC
  • Wasu Masu Kyamar Musulunci Sun Kai Hari Kan Masallaci A Sweden

Wasu masu tsananin kyamar musulunci sun kai hari kan wani masallaci a unguwar Ringby da ke cikin birnin Stockholm fadar mulkin kasar Sweden.

Kamfanin dillancin labaran Anatoly ya bayar da rahoton cewa, wasu mutane da ba a san ko su wane ne ba suka kai harin a kan wannan masallaci, wanda yake hade da wata babbar cibiyar musulunci, inda suka yi barna tare da farfasa tagogi da lalata wasu kayayyakin masallacin, kuma suka tsere ba tare da kame ko daya daga cikinsu ba.

A nasu bangaren mahukuntan kasar ta Sweden sun bayyana rashin jin dadi dangane da faruwar lamarin, a daidai lokacin da jami'an tsaro suka sanar da cewa sun shiga gudanar da bincike kan lamarin, da zimmar kame duk wadanda suke da hannu a cikin wannan aika aika, domin gurfanar da su a gaban kuliya.

Kimanin musulmi dubu 400 ne dai suke rayuwa a cikin kasar Sweden, kuma ba su cika fuskar matsaloli irin wadannan ba daga jama'ar gari, sai bayan da aka fara samun hare-haren ta'addanci daga 'yan takfiriyyah a cikin kasashen turai.