-
Shugaban Colombia Juan Manuel Santos Ya Lashe Kyautar Nobel Na Zaman Lafiya
Oct 07, 2016 14:55An sanar da shugaban kasar Colombia Juan Manuel Santos a matsayin wanda ya lashe kyautar Nobel ta zaman lafiya na shekara ta 2016 sakamakon kokarinsa wajen cimma yarjejeniyar sulhu da 'yan tawayen Farc na kasar duk kuwa da rudanin da ke tattare da yarjejeniyar a halin yanzu.
-
Majalisar Duma Ta Amince Da Yarjejeniyar Ci Gaba Da Zaman Sojojin Saman Rasha A Siriya
Oct 07, 2016 14:55Majalisar wakilan kasar Rasha (Duma) ta amince da yarjejeniyar da aka cimma tsakanin gwamnatocin kasashen Rasha da Siriya na ci gaba da zaman sojojin saman kasar Rashan a Siriya na tsawon lokacin da ba a iyakance shi ba.
-
Yawan Mutanen Da Suka Rasa Rayukansu Sanadiyyar Guguwar Iska A Kasar Haiti Ya Kai 339.
Oct 07, 2016 06:38Yawan mutanen da suka rasa rayukansu a guguwar iska hade da ruwan sama a kasar Haiti ya kai 339.
-
Wani Bom Ya Tashe Kusa Da Wani Ofishin Yansanda A Istambul NA Kasar Turkiya Ya Raunata Mutane 10
Oct 06, 2016 14:21Akalla mutane goma ne suka ji rauni a lokacinda wani bom da aka dana a jikin babur ya tashi kusa da wani ofishin yansanda a birnin Istambul na kasar turkia a safiyar yau Alhamis.
-
Dubban Mayakan Kungiyoyin Yan Ta'adda A Kasashen Iraqi Da Syria Sun Fito Ne Daga Kasashen Turai
Oct 06, 2016 13:52Ministan harkokin wajen kasar Austria ya bayyana cewa dubban mayakan kungiyoyin yan ta'adda a kasar Iraqi da Syria sun fito ne daga kasashen tarayyar Turai.
-
Gwamnatin Kasar Libya Ta Ki Amincewa Da Kafa Sansanin Yan Gudun Hijira Zuwa Turai A Cikin Kasarta
Oct 06, 2016 12:36Ministan harkokin wajen kasar Libya Tahar Sayyalah ya bada sanarwan cewa gwamnatin kasar ba zata amincewa kasashen turai su kafa sansanin yan gudun hijira zuwa kasashen na Turai cikin kasarsa ba.
-
Mahaukaciyar Guguwar 'Mathew' Ta Hallaka Mutane 23 A Kasar Haiti
Oct 06, 2016 07:27Mahaukaciyar guguwa da ta haifar da ambaliyar ruwa da aka ba wa suna "Matthew" ta kashe mutane 27 a kasar Haiti da Jamhuriyar Dominican yayin da mutanen kuma sun bace babu labarinsu.
-
Jamus Za Ta Kafa Sansanin Soji A Nijar
Oct 06, 2016 02:25Kasar Jamus za ta gina wani sansanin soji a Jamhuriyar Nijar domin fada da ayyukan ta’addanci a makofciyar kasar Mali.
-
EU Ta Kudiri Anniyar Yaki Da Kwararar Bakin Haure
Oct 06, 2016 02:23Kungiyar tarayya turai ta EU, ta kaddamar da wata sabuwar rundunar jami'an tsaron iyakoki domin kara karfafa matakanta na yaki da kwararar bakin haure.
-
Kasar Rasha Ta Yi Tayin Shiga Tsakani Don Magance Rikicin Kasar Libiya
Oct 05, 2016 07:29A karon farko kasar Rasha ta yi tayin shiga tsakani a tattaunawar sulhu tsakanin bangarorin da ba sa ga maciji da juna na kasar Libiya da nufin kawo karshen rikicin kasar da ya ki ci ya ki cinyewa.