Jamus Za Ta Kafa Sansanin Soji A Nijar
https://parstoday.ir/ha/news/world-i12052-jamus_za_ta_kafa_sansanin_soji_a_nijar
Kasar Jamus za ta gina wani sansanin soji a Jamhuriyar Nijar domin fada da ayyukan ta’addanci a makofciyar kasar Mali.
(last modified 2018-08-22T06:59:02+00:00 )
Oct 06, 2016 02:25 UTC
  • Jamus Za Ta Kafa Sansanin Soji A Nijar

Kasar Jamus za ta gina wani sansanin soji a Jamhuriyar Nijar domin fada da ayyukan ta’addanci a makofciyar kasar Mali.

Jakadan kasar ta Jamus ne a Nijar, Bernd von Munchow-Pohl, ya bayyana hakan a wani jawabi a game da zagayowar ranar da aka hade Jamus ta gabas da kuma yamma.

Jamus ta ce wannan sasanin zai karfafa aikin tawagar  MINUSMA dake yaki da mayakan jihadi a kasar Mali.

A 'yan kwanaki masu zuwa ne ake sa ran shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel zata ziyarci kasar ta Nijar

Wannan dai na zuwa ne kwanaki kadan bayan da Amurka ta sanar da cewa tana gina wani sansanin soji na jirage masu sarafa kansu a arewacin kasar ta Nijar.

Kafin hakan dai dama faransa ta kwashe shekaru hudu tana aikin soji a kasar ta Nijar.

kungiyoyin fara hula da dama ne a kasar ta Nijar suka soki lamarin gwamnatin kasar dangane da baiwa kasashen yamma damar kafa sansanin soji wanda a cewarsu ya keta yancin da kasar take dashi.