EU Ta Kudiri Anniyar Yaki Da Kwararar Bakin Haure
https://parstoday.ir/ha/news/world-i12043-eu_ta_kudiri_anniyar_yaki_da_kwararar_bakin_haure
Kungiyar tarayya turai ta EU, ta kaddamar da wata sabuwar rundunar jami'an tsaron iyakoki domin kara karfafa matakanta na yaki da kwararar bakin haure.
(last modified 2018-08-22T06:59:02+00:00 )
Oct 06, 2016 02:23 UTC
  • EU Ta Kudiri Anniyar Yaki Da Kwararar Bakin Haure

Kungiyar tarayya turai ta EU, ta kaddamar da wata sabuwar rundunar jami'an tsaron iyakoki domin kara karfafa matakanta na yaki da kwararar bakin haure.

Wannan rundinar zata gaji aikin rundinar Frontex dake kan iyaka kasashen Bulgeriya da Turkiyya hanyar da bakin hauren suka fi amfani da ita wajen shiga Turai.

Daya daga cikin aikin wannan rundinar shi ne taimakawa kasashen da bakin hauren ke yada zango a lokacinda kwararen bakin hauren ta tsananta.

Rundinar dai ta kunshi mutane 1,500 na kasashe mambobin kungiyar da za'a iya neman agajinsu a duk lokacinda bukatar hakan ta taso.

Al'kaluma sun nuna cewa a shekara 2015 data gabata sama da bakin haure 850,000 suka isa Girka ta teku, galibinsu kuma na yankin gabas ta tsakiya ne da Asiya dake gujewa rikice rikice a kasashensu.