Pars Today
Babban sakataren majalisar tsaron kasar Rasha ya bayyana cewa, Amurka na shirye-shiryen kaddamar da harin soji a kan kasar Venezuela, da nufin kifar da gwamnatin kasar.
Kasar Pakistan ta sanar da kakkabo wasu jiragen yakin sojin kasar India guda biyu da tace sun keta sararin samaniyarta.
Wata kotu a kasar Australia ta tabbatar da laifin cin zarafin yara biyar a kan wani babban jami'an cocin Catholica
Gungun kasashen Latine Amurka na Lima dake adawa da mulkin shugaba Nicolas Maduro, sun kalubalanci duk wani yunkuri na yi amfani da karfi kamar yadda Amurka take shirin yi a kasar Venezuela.
A kalla mutane 150 ne suka mutu sanadiyyar shan barasa a arewa maso gabacin kasar India, karo na biyu kenan a cikin wata guda.
Sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo ya fada a jiya Lahadi cewa Amurka za ta sanya karin takunkumi kan kasar Venezuela.
Shugaban kasar Iraki, Barham Saleh, ya fara wata ziyarar aiki ta kwanaki biyu a Faransa.
Shugabann Amurka Donald Trump, ya wallafa a shafinsa na Tweeter cewa, zai jinkirta amfani da karin haraji kan kayayyakin da kasar Sin ke shigarwa kasarsa da aka shirya fara amfani da shi a ranar 1 ga watan Maris.
Shugaban hukumar abinci da magani na jamhuriyar musulunci ta Iran Mhedi Pirsalehi ne ya bayyana haka a yayin wata ganawa da ya yi da tawagar kasar Venezuela wacce mataimakin ministan harkokin wajen kasar yake jagoranta.
Shugaba Donald Trump, na Amurka ya nada jami'ar diflomatsiyar kasar, Kelly Knight Craft, a matsayin sabuwar jekadiyar kasar a MDD.