Feb 27, 2019 18:20 UTC
  • Rasha ta Ce Amurka Na Shirin Kai Wa Kasar Venezuela Harin Soji

Babban sakataren majalisar tsaron kasar Rasha ya bayyana cewa, Amurka na shirye-shiryen kaddamar da harin soji a kan kasar Venezuela, da nufin kifar da gwamnatin kasar.

Kamfanin dilalncin labaran IRNA ya bayar da rahoto cewa, Nikolai Patrushev babban sakataren majalisar tsaron kasar Rasha ya fadi a jiya cewa, yanzu haka Amurka na shirye-shiryen kaddamar da harin soji a kan kasar Venezuela, domin kawo karshen gwamnatin shugaba Nicolas Maduro wanda ba ya dasawa da kasar ta Amurka.

Tun kafin wannan lokacin dai gwamnatin kasar Rasha ta yi gargadi kan take-taken an Amurka, inda a baya ta shirya juyin mulki a kasar ta Venezuela wanda bai yi nasara ba, bayan nan kuma Amurka ta yi amfani da wasu 'yan adawar siyasa da take mara ma baya a kasar ta Venezuela da nufin jefa kasar cikin rikici, inda har yanzu take ci gaba da tunzura su da kuma ba su makamai, baya ga haka kuma tana ci gaba da jibge sojoji a cikin kasar Columbia, a kan iyakar kasar da Venezuela.

Kasashen duniya da dama musamman masu 'yancin siyasa daga cikinsu, duk suna yi tir da Allawadai da wanann wutar fitina da Amurka ta kunna a kasar Venezuela, da nufin  jefa kasar cikin yakin basasa.

Tags