Iran A Shirye Take Ta Aike Da Magunguna Zuwa Venezuela
https://parstoday.ir/ha/news/world-i35345-iran_a_shirye_take_ta_aike_da_magunguna_zuwa_venezuela
Shugaban hukumar abinci da magani na jamhuriyar musulunci ta Iran Mhedi Pirsalehi ne ya bayyana haka a yayin wata ganawa da ya yi da tawagar kasar Venezuela wacce mataimakin ministan harkokin wajen kasar yake jagoranta.
(last modified 2019-02-24T09:39:26+00:00 )
Feb 24, 2019 09:37 UTC
  • Iran A Shirye Take Ta Aike Da Magunguna Zuwa Venezuela

Shugaban hukumar abinci da magani na jamhuriyar musulunci ta Iran Mhedi Pirsalehi ne ya bayyana haka a yayin wata ganawa da ya yi da tawagar kasar Venezuela wacce mataimakin ministan harkokin wajen kasar yake jagoranta.

Ganawar da bangarorin biyu su ka yi, tana a karkashin yarjejeniyar fahimtar juna ta aiki da kasashen biyu su ka rattabawa hannu a shekarar da ta gabata akan harkar abinci da magani.

A yayin taron, Mhedi Pirsalehi ya bayyana cewa Iran a shirye tyake ta aike da magunguna da kuma kayan aiki na asibiti zuwa kasar ta Venezuela.