Pars Today
Mataimakin shugaban kasar Amurka Mike Pence ya gargadi kungiyar tarayyar Turai kan ko su zabi kasancewa da Amurka ko kuma tare da yarjejeniyar Nukliyar da suka kulla da Iran.
Emmanuel Macron shugaban kasra Faransa ya tattauna ta wayan tarho da takwaransa na kasar Amurka Donald Trump inda ya bayyana masa muhimmancin ci gaba da mutunta yerjejeniyar nukliya tsakanin Iran da Kasashe 5+1.
Shugaban Ofishin Siyasa na Shugaban kasar Jamhuriyar musulinci ta Iran ya ce shakka babu idan Amurka ta fice daga yarjejjeniyar da Iran ta cimma kan shirinta na nukiliya na zaman lafiya za ta yi nadama kuma za ta cutu fiye da kasar Iran.
Ma'aikatar harakokin wajen Amurka ta sanar a ranar Talata cewa a ranar Juma'a mai zuwa shugaba Donald Trump zai bayyana matsayarsa a game da yarjejjeniyar da Iran ta cimma da kasashen duniya kan shirinta na nukiliya na zaman lafiya.
Tsohon ministan makamashi na kasar Amurka, Ernest Moniz ne ya gargadin gwamnatin kasarsa akan abinda zai biyo bayan ficewar Amurka daga cikin yarjejeniyar
Wakilan majalisar dokokin kasar Amurka 24 yan jam'iyyar Republican sun rubuta wasika zuwa gwamnatin shugaba Donald Trump kan abin da suka kira sabuwar yarjejeniyar Nukliyan da kasar Iran ta yi.
Shugaban kwamitin tsaron kasa a majalisar dokokin kasar Iran ya ce Iran tana amfana da yerjejeniyar da ta cimma da manyan kasashen duniya kan shirinta na makamashin nukliya duk tare da adawar da Amurka take nunawa.
Ministan harkokin wajen Birtaniya da yake ziyarar aiki a Iran, ya tabbatarwa da takwaransa na Iran Muhammad Jawad Zarif cewa; Kasarta tana aiki da yarjejeniyar ta Nukiliya
Ministan harkokin wajen kasar Iran Mohammad Jawad Zarif ya bayyana cewa sojojin kasar Iran sun shiga kasar Siria ne tare da bukatar gwamnatin kasar.
Wani masharhanci kan harkokin siyasar Amurka ya ce: Mafi yawan Amurkawa ba su goyon bayan bakar siyasar shugaban kasar Donald Trupm kan kasar Iran musamman kokarinsa na rusa yarjejeniyar nukiliya da aka cimma tsakanin Iran da manyan kasashen duniya.