Zarif : Iran Ta Shiga Siriya Ne Da Bukatar Gwamnatin Kasar
(last modified Fri, 01 Dec 2017 06:23:31 GMT )
Dec 01, 2017 06:23 UTC
  • Zarif : Iran Ta Shiga Siriya Ne Da Bukatar Gwamnatin Kasar

Ministan harkokin wajen kasar Iran Mohammad Jawad Zarif ya bayyana cewa sojojin kasar Iran sun shiga kasar Siria ne tare da bukatar gwamnatin kasar.

Kamfanin dillancin Larabaran IRNA daga birnin Roma na kasar Italia, ya nakalto Zarif yana fadar haka a jiya Alhamis a lokacinda yake halattan taron kasa da kada ta Medeteranian. Zarif ya kara da cewa a shekara ta 2011 ne kungiyoyin yan ta'adda masu samun goyon bayan Amurka, Saudia da kuma kawayensu a yankin, suka mamaye yankuna da dam a kasashen Iraqi da Siria.

A nan ne gwamnatin kasar Siria ta neman Taimakon Iran da Rasha don fuskantar wadan nan yan ta'adda, wadanda suka hada da kungiyar Daesh kuma  ta Jibhatun Nusra.

Ministan ya kara da cewa gwamnatin kasar Saudia tana tsammani ta hanyar sayan Makamai daga kasashen yamma ne zata samarwa kanta da kuma yankun zaman lafiya. Banda haka, kasar ta saudia ta ki amincewa da dukkan hanyoyin dawo da zaman lafiya a kasashen yankin ta hanyar tattaunawa. .

Dangane da yerjejeniya  shirin Nukliyar kasar Iran kuma Zarif ya bayyana cewa yerjejeniya ce mai kyau wacce yakamata dukkan bangarorin da abin ya shafa su kiyayeta, amma gwamnatin Amurka wacce bangare ce a yerjejeniyar tana kokarin ganin yerjejeniyar bata kai labari ba.