Boris Johnson: Birtaniya Tana Aiki Da Yarjejeniyar Nukiliya Da Iran
Ministan harkokin wajen Birtaniya da yake ziyarar aiki a Iran, ya tabbatarwa da takwaransa na Iran Muhammad Jawad Zarif cewa; Kasarta tana aiki da yarjejeniyar ta Nukiliya
Bugu da kari, Johnson ya bukaci ganin an sami fadada da bunkasar alaka a tsakanin Iran da Birtaiya ta fuskoki da dama.
Har ila yau, ministan harkokin wajen na Birtaniya da takwaransa na Iran sun tattauna hanyoyi daban-daban na alakar kasashen biyu musamman tattalin arziki da huldar Bankuna da kuma kasuwanci.
A jiya asabar ministan harkokin wajen na Birtaniya ya gana da shugaban majalisar shawarar musulunci ta Iran Dr, Ali Larijani. Kuma a yayin wannan ziyarar ta Boris Johnson zai gana da shugaban kasa Dr. Hassan Rauhani da kuma shugaban hukumar makamashin Nukiliya ta kasa Ali Akbar Salihi.