Pars Today
Babban magatakardar Majalisar Dinkin Duniya António Guterres ya ci gaba da cewa wajibi ne a kiyaye yarjejeniyar saboda kare zaman lafiya a duniya.
Shugaban hukumar gudanarwa ta kungiyar tarayyar Afrika (AU) ya sanar da cewa: Kungiyar Tarayyar Afrika tana jaddada goyon bayanta kan yarjejeniyar nukiliya da aka cimma tsakanin kasar Iran da manyan kasashen duniya a shekara ta 2015.
Babbar jami'ar harkokin wajen kungiyar Tarayyar Turai Federica Mogherini ta bayyana cewar yarjejeniyar nukiliyan kasar Iran wata nasara ce ga duniya da kuma al'ummar Iran wanda wajibi ne a kiyaye da kuma ci gaba da aiwatar da ita.
Shugaban hukumar gudanarwa ta Tarayyar Afirka (AU), Moussa Faki Mahamat, ya sanar da cewa kungiyar Tarayyar Afirkan tana goyon bayan yarjejeniyar nukiliya da manyan kasashen duniya suka cimma da Iran a shekara ta 2015.
Ministocin harkokin wajen kungiyar Tarayyar Turai sun sanar da cikakken goyon bayansu ga yarjejeniyar nukiliyan da aka cimma da Iran suna masu cewa kasashensu za su ci gaba da aiki da abin da aka cimma cikin yarjejeniyar.
Shugaban kungiyar tarayyar Afirkan ya ce; Kungiyarsa tana bada cikakken goyon bayanta ga yarjejeniyar.
Shugaban kasar Faransa ya bayyana cewa: Ra'ayin kasarsa ya sha bamban da na Amurka kan Jamhuriyar Musulunci ta Iran, kuma zai samu lokaci da ya dace domin gudanar da ziyarar aiki a kasar ta Iran.
Babban kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musuluci na Iran (IRGC) Manjo Janar Muhammad Ali Jafari ya bayyana cewar bakin dakarun kare juyin juya halin Musuluncin na Iran da na Ma'aikatar harkokin wajen kasar sun zo daya a fagen kare manufofin juyin juya halin Musulunci yana mai kiran shugaban Amurka da ya fahimci hakan.
Shugaban hukumar Makamashin nukliya na kasar Iran Ali Akbar Salihi ya bayyana cewa babu wata sabuwar tattaunawa kan shirin makamashin nukliyar kasar.
Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya ya jaddada muhimmancin kiyaye yarjejeniyar nukiliyar da aka cimma tsakanin kasar Iran da manyan kasashen duniya biyar gami da kasar Jamus.