Kungiyar Tarayyar Afirka Ta Bayyana Goyon Bayanta Kan Yarjejeniyar Nukiliyan Iran
Shugaban hukumar gudanarwa ta Tarayyar Afirka (AU), Moussa Faki Mahamat, ya sanar da cewa kungiyar Tarayyar Afirkan tana goyon bayan yarjejeniyar nukiliya da manyan kasashen duniya suka cimma da Iran a shekara ta 2015.
Kamfanin dillancin labaran ISNA na Iran ya bayyana cewar a yau ne Shugaban hukumar gudanarwa ta Tarayyar Afirka (AU), Moussa Faki Mahamat ya sanar da hakan inda ya ce Kungiyar Tarayyar Afirkan tamkar sauran kungiyoyi na kasa da kasa sun yi maraba da yarjejeniyar nukiliyan sannan kuma suna ganinta a matsayin nasarar tafarkin diplomasiyya da kuma magance matsalolin da suka kunno kai ta hanyar tattaunawa.
Har ila yau Mr. Mahamat ya ce wajibi ne kowa da kowa ya girmama yarjejeniyar nukiliyan a matsayinta na wata yarjejeniya da hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya ta amince da ita.
Sanarwar kungiyar Tarayyar Afirkan dai tana a matsayin mayar da martani ne ga shugaban Amurka Donald Trump wanda ya ce bai amince da yarjejeniyar ba, sannan kuma akwai yiyuwar ma Amurka ta yi watsi da ita.