Tarayyar Afirka Tana Goyon Bayan Yarjejeniyar Nukiliyar Iran.
Shugaban kungiyar tarayyar Afirkan ya ce; Kungiyarsa tana bada cikakken goyon bayanta ga yarjejeniyar.
Musa Fakky Muhammad wanda ya fitar da bayani da sunan tarayyar ya ci gaba da cewa; Daidai da sauran kungiyoyin kasa da kasa tarayyar ta goyi bayan yarjejeniyar da aka cimmawa akan shirin Nukiliyar Iran, tare da bayyana shi a matsayin nasarar dipomasiyya.
Shugaban cibiyar tarayya turai din ya ci gaba da cewa; Da akwai bukatar dukkanin bangarorin yarjejeniyar da su girmamata.
A ranar juma'ar da ta gabata ne dai shugaban kasar Amurka ya yi bayani akan yarjejeniyar wanda ya bayyana a matsayin mafi muni ga Amurka.
Sai dai kasashen duniya sun yi watsi da jawabin nashi tare da bayyana cigaba da goyon bayansu ga yarjejeniyar.