-
Ruhani: Matsayar Trump Kan Qudus Zai Sake Haifar Da Rikici Ne A Gabas Ta Tsakiya
Dec 13, 2017 05:47Shugaban kasar Iran Dakta Hasan Ruhani yayi kakkausar suka ga matsayar da shugaban Amurka Donald Trump na sanar da Qudus a matsayin helkwatar haramtacciyar kasar Isra'ila yana mai cewa babu abin da hakan zai haifar in ban kirkiro wani sabon rikici a yankin Gabas ta tsakiya.
-
Wasu Kasashen Larabawa Sun Fitar Da Daftarin Kuduri Kan Matakin Donald Trump Dangane Da Birnin Qudus
Dec 12, 2017 11:58Jakadun wasu kasashen Larabawa sun fitar da daftarin kuduri kan matakin da shugaban kasar Amurka ya dauka dangane da birnin Qudus suna neman tsoma bakin kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya da babban zauren Majalisar.
-
Vatican: Matakin Trump Dangane Da Birnin Quds Zai Kara Dagula Lamurra Ne Kawai
Dec 11, 2017 11:51Tsohon ministan harkokin waje na Vatican Pietro Parolin ya bayyana cewa matakin da shugaban kasar Amurka Donald Trump ya dauka kan birnin Quds zai kara rikita harkokin zaman lafiya a yankin gabas ta tsakiya ne.
-
Bayanin Bayan Taron Kasashen Larabawa Akan Kudus
Dec 10, 2017 07:34Da safiyar yau lahadi ne kasashen taron gaggawa na ministocin harkokin wajen kasashen larabawa ya fitar da bayani da ya kunshi yin tir da matakin shugaban kasar Amurka akan birnin kudus
-
Shugaban Kiristoci Kibdawa Na Masar Ya Soke Ganawa Da Mataimakin Shugaban Amurka Saboda Batun Qudus
Dec 09, 2017 17:00Paparoman Kibdawan kasar Masar, Paparoma Tawadros II ya soke shirin ganawa da mataimakin shugaban kasar Amurka Mike Pence da a baya aka shirya yi a wani lokaci a watan nan a birnin Alkahira don nuna rashin amincewarsa ga matsayar da shugaban Amurkan ya dauka na bayyanar birnin Qudus a matsayin babban birnin haramtacciyar kasar Isra'ila.
-
Martanin Jaridun Kasashen Turai Kan Matakin Da Gwamnatin Amurka Ta Dauka A Kan Quds
Dec 07, 2017 11:46Jaridun kasashen Turai sun yi suka kan matakin da gwamnatin kasar Amurka ta dauka na amincewa da birnin Quds a matsayin cibiyar gwamnatin HKI.
-
Iran Ta Yi Allah Wadai Da Sanarwar Trump Na Bayyanar Kudus A Matsayin Helkwatar 'Isra'ila'
Dec 07, 2017 05:54Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta yi kakkausar suka da kuma Allah wadai da matsayar da shugaban Amurka Donald Trump ya dauka na mayar da ofishin jakadancin Amurka birnin Quds a matsayin babban birnin haramtacciyar kasar Isra'ila yana tana mai cewa hakan wani lamari ne da zai kunna wutar sabon boren intifada a kasar Palastinun.
-
Ruhani Ya Ja Kunnen Amurka Kan Mayar Da Ofishin Jakadancinta Birnin Qudus
Dec 07, 2017 05:52Shugaban kasar Iran Dakta Hasan Ruhani ya ja kunnen Amurka dangane da batun mayar da ofishin jakadancinta zuwa birnin Qudus yana mai cewa wajibi ne kasashen musulmi su hada kansu waje guda don tinkarar wannan lamari.
-
Ruhani: Amurka Tana Haifar Da Fitina Ne Don Cika Aljihunta Daga Dukiyar Gabas Ta Tsakiya
Nov 08, 2017 11:20Shugaban kasar Iran Dakta Hasan Ruhani ya bayyana cewar a koda yaushe manyan kasashen duniya musamman Amurka suna kokari wajen haifar da rikici da yake yake a yankin Gabas ta tsakiya don haka ya kirayi shugabannin wasu kasashen yankin da su fahimci hakan da kuma yin aiki tukuru wajen tabbatar da hadin kai da fahimtar juna a tsakanin al'ummomin kasashen yankin.
-
Kwamandan IRGC Ya Musanta Zargin Trump Na Cewa Iran Tana Da Hannu Cikin Makamin Da Aka Harba Saudiyya Daga Yemen
Nov 05, 2017 18:14Babban kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musulunci na kasar Iran Manjo Janar Muhammad Ali Jaafari ya bayyana maganganun shugaban Amurka Trump cewa Iran tana da hannu cikin makami mai linzami da aka harba daga Yemen zuwa Saudiyya a matsayin karya tsagoronta.