Nov 08, 2017 11:20 UTC
  • Ruhani: Amurka Tana Haifar Da Fitina Ne Don Cika Aljihunta Daga Dukiyar Gabas Ta Tsakiya

Shugaban kasar Iran Dakta Hasan Ruhani ya bayyana cewar a koda yaushe manyan kasashen duniya musamman Amurka suna kokari wajen haifar da rikici da yake yake a yankin Gabas ta tsakiya don haka ya kirayi shugabannin wasu kasashen yankin da su fahimci hakan da kuma yin aiki tukuru wajen tabbatar da hadin kai da fahimtar juna a tsakanin al'ummomin kasashen yankin.

Shugaba Ruhani ya bayyana hakan ne a yayin da yake gabatar da jawabi wajen taron majalisar ministocinsa inda yayin da yake magana kan kokarin da wasu kasashen yankin Gabas ta tsakiya musamman Saudiyya suke yi wajen haifar da rikici tsakanin al'ummomin yankin ya bayyana cewar Amurka da sauran manyan kasashen yammaci suna kokarin haifar da fitina din ne don su sami damar sayar da makamansu kawai.

Yayin da ya koma kan irin adawar da mahukutar Saudiyya suke nuna wa Iran, shugaba Ruhani ya ce wani amfani Saudiyya za ta samu daga kokarin da take yi na nuna kiyayya da adawa da wasu kasashen yankin Gabas ta tsakiyan.

Shugaba Ruhani ya kara da cewa: Idan ma har abin a dauka Saudiyya tana kiyayya da al'ummar Iran, to mene ne dalilinta na adawa da mutanen Yemen har take musu ruwan bama-bamai alhali kuwa su din makwabtanta ne? Shugaban na Iran ya kirayi Saudiyya ta dakatar da irin wadannan hare-haren da take kai wa al'ummar Yemen din ta gani ko su ma ba za su daina kai mata hare-hare ba.

Shugaban na Iran dai ya kirayi Saudiyya da ta kawo karshen goyon bayan 'yan ta'adda da take yi a Iraki da Siriya kamar yadda kuma ya kiraye ta da ta yi kokarin magance matsalolinta na cikin gida ba tare da ta shigo da wasu kasashe ciki ba.

Tags