-
Kokarin Amurka Da Kawayenta Na Cutar Da Iran A Kwamitin Tsaron MDD
Feb 24, 2018 06:00A kokarin da suke yi wajen wasa da hankulan al'ummomin duniya kan irin rawar da suke takawa a ci gaba da kisan kiyashin da ake yi wa al'ummar Yemen, kasashen Amurka, Birtaniyya da Faransa na ci gaba da kokari wajen amfani da Kwamitin Tsaron MDD wajen tuhumar Iran da aikewa da makamai kasar Yemen.
-
Hukumar IAEA Ta Ce: Iran Tana Ci Gaba Da Mutunta Yarjejeniyar Nukiliya
Feb 23, 2018 05:30A wani sabon rahoton da hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya ta IAEA ta fitar ya jaddada cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran tana ci gaba da mutunta yarjejeniyar makamashin nukiliya da aka cimma da ita.
-
Araqchi: Iran Za Ta Fice Daga Yarjejeniyar Nukiliya Idan Ya Zamana Babu Amfanin Da Take Samu
Feb 22, 2018 17:40Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta bayyana cewar za ta fice daga yarjejeniyar nukiliya matukar dai ya zamana ba ta amfanuwa da wani abu daga cikin abin da aka cimma sakamakon barazanar da Amurka take ci gaba da yi wa kamfanoni da cibiyoyin musayen kudade da suke son mu'amala da ita.
-
Ruhani: Babu Kofar Tattaunawa Kan Makaman Tsaron Kasa
Feb 22, 2018 11:54Shugaba Ruhani na kasar Iran ya bayyana cewa makamai masu linzami na kasar Iran ba zai taba zama abin tattaunawa a kansa ba.
-
Rasha Ta Hana Wucewar Wani Daftarin Kudirin Yin Allah Wadai Da Iran Kan Kasar Yeman A Komitin Tsaro
Feb 22, 2018 11:52Jakadan kasar Rasha a majalisar dinkin duniya ya hana wani daftarin kuduri wanda kasashen yamma suka gabatar na yin Allah wadai da kasar Iran a kan kasar Yeman.
-
Adawar Rasha Kan Kakabawa Iran Takunkumi A Kwamitin Tsaron MDD.
Feb 22, 2018 05:31Wakilin kasar Rasha a Majalisar dinkin duniya ya ce ba za su amince da duk wani kokari da kwamitin tsaron Majalisar dinkin duniya ke yi na kakabawa Iran takunkumi ba, bisa zarkin tana baiwa kungiyar Ansarullah ta kasar yemen makamai
-
An Shiga Mataki Na Karshe A Binciken Sauran Gawawwakin Wadanda Suka Rasu A Hadarin Jirgi A Iran
Feb 21, 2018 17:43Mataimakin hukumar bayar da agajin gaggawa ta Hilal Ahmar a kasar Iran Shahin Fathi ya bayyana cewa, a yau Laraba an shiga mataki na karshe na kokarin tattara sauran gawwakin da suka bata a cikin dusar kankara, sakamakon hadarin jirgin fasinja da ya auku a kasar.
-
An Gano Bubucin Jirgin Da Ya Fadi Da Kuma Gawakin Fasinjoji A Kan Tsaunuka Rufe Da Dussan Kankara A Kasar Iran
Feb 20, 2018 11:57Jami'an tsaron kasar Iran na dakarun kare juyin juya halin musulunci sun bada labarin gano burbushin jirgin saman fasinjan da ta yi hatsari a kan tsaunukan Zogros a ranar lahadi da ta gaba da kuma gawakin fasinjoji a inda jirgin ya fadi.
-
Ana Ci Gaba Da Gudanar Da Ayyukan Binciken Jirgin Saman Da Ya Fado A Iran
Feb 19, 2018 11:03Mahukunta a kasar Iran sun bayyana cewar an tura sama da kwararrun hawa duwatsu 100 tare da wasu jami'an ba da agaji da dama yankin da ake tsammanin jirgin saman daukar fasinjoji na kasar ya fadi a jiya don ci gaba da bincike da gano buraguzan jirgin duk kuwa da matsalar rashin kyawun yanayi da ake fuskanta.
-
Kungiyar Tarayyar Turai Ta Yi Ta'aziyyar Mutanen Da Suka Rasa Rayukansu A Hadarin Jirgi A Iran
Feb 19, 2018 06:29Kungiyar tarayyar turai ta fitar da bayanin ta'ziyya dangane da rasuwar mutane 66 a wani hadarin jirgi da ya faru jiya a kasar Iran.