Hukumar IAEA Ta Ce: Iran Tana Ci Gaba Da Mutunta Yarjejeniyar Nukiliya
A wani sabon rahoton da hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya ta IAEA ta fitar ya jaddada cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran tana ci gaba da mutunta yarjejeniyar makamashin nukiliya da aka cimma da ita.
A jawabin da babban sakataren hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya Yukiyo Amano ya gabatar a jiya Alhamis kan sabon rahoton hukumarsa ya jaddada cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran tana ci gaba da kiyaye dukkanin yarjejeniyar da aka cimma da ita kan shirinta na makamashin nukiliya na zaman lafiya, kuma tuni kasar Iran ta sanar da hukumar ta IAEA shirinta na samar da cibiyar makamashin nukiliya a karkashin ruwa.
Amano ya kara da cewa: Dukkanin shirye-shiryen makamashin nukiliyar Iran musamman tace karfen yuraniyon suna gudana ne kan sanya idon hukumarsa ta IAEA.