Adawar Rasha Kan Kakabawa Iran Takunkumi A Kwamitin Tsaron MDD.
https://parstoday.ir/ha/news/world-i28445-adawar_rasha_kan_kakabawa_iran_takunkumi_a_kwamitin_tsaron_mdd.
Wakilin kasar Rasha a Majalisar dinkin duniya ya ce ba za su amince da duk wani kokari da kwamitin tsaron Majalisar dinkin duniya ke yi na kakabawa Iran takunkumi ba, bisa zarkin tana baiwa kungiyar Ansarullah ta kasar yemen makamai
(last modified 2018-08-22T11:31:27+00:00 )
Feb 22, 2018 05:31 UTC
  • Adawar Rasha Kan Kakabawa Iran Takunkumi A Kwamitin Tsaron MDD.

Wakilin kasar Rasha a Majalisar dinkin duniya ya ce ba za su amince da duk wani kokari da kwamitin tsaron Majalisar dinkin duniya ke yi na kakabawa Iran takunkumi ba, bisa zarkin tana baiwa kungiyar Ansarullah ta kasar yemen makamai

Hukumar gidan talabijin da radio na kasar Iran ya nakalto Vasily Nebenzya wakilin kasar Rasha a MDD yayin da yake kalubalantar yunkurin kasashen yamma na yin alawadai da kan kasar Iran bisa zarkin taimakawa mayakan Ansarullah na kasar yemen da makamai a jiya laraba na cewa bai kamata ba kwamitin tsaron MDD ya hukunta kasar Iran a kudirin sabunta takunkumi kan kasar Yemen.

A halin da ake ciki, kwamitin tsaron na cikin tattauanawa kan wani sabon kudiri da kasar Birtaniya ta gabatar tare da shawarar kasashen Amirka da Faransa, da a cikinsa za a hukunta kasar Iran bisa zarkinta da taimakawa mayakan kungiyar gwagwarmaya na Ansarullah na kasar Yemen, Rasha ta bayyana wannan kudiri da ake sa ran za a kada kuri'a kansa a ranar 26 ga watan Favrayu, da abinda ba za ta amince da shi ba.