-
Iran Ta Bukaci Amurka Da Ta Dakatar Da Sayar Da Makamai Ga 'Masu Goyon Bayan Ta'addanci"
May 23, 2017 05:53Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta kirayi Amurka da ta yi watsi da siyasarta ta neman hada fada, tsoma baki cikin harkokin cikin gidan kasashe, sanya tsoron Iran cikin zukatan kasashe da kuma sayar da makamai masu hatsari da manyan masu goyon bayan ayyukan ta'addanci a duniya.
-
Zarif: Zai Fi Kyau Ga Trump Ya Kula Kada A Sake Kai Musu Hari Irin Na 9/11
May 21, 2017 17:19Ministan harkokin wajen kasar Iran Muhammad Jawad Zarif, ya ja hankalin shugaban kasar Amurka Donald Trump da cewa, da zai fi a gare shi a ziyarar da yake yi a saudiyya ya tabbatar da cewa sun daddale da mahukuntan kasar, domin kada a sake kai ma Amurka wani hari makamancin 9/11.
-
Dan Kasar Iran Ya Zo Na Daya A Gasar Kur’ani Ta Duniya A Malaysia
May 21, 2017 17:18Makarancin kur'ani mai tsarki dan kasar Iran Hamed Alizadeh ya zo na daya a gasar karatun kur'ani mai tsarki ta duniya karo na 59 a kasar Malaysia .
-
Shugabanin Kasashen Duniya Na Ci Gaba Da Yiwa Shugaba Ruhani Murnar Samun Nasara A Zabe
May 21, 2017 07:34Shugaban Kasar Faransa Emmaniel Macron ya aike da sakon murna ga Shugaban kasar Iran Dr Hasan Ruhani dangane da nasarar da ya samu a zaben Shugabancin kasar
-
Vilayati:Halartar Mutane Shine Tushen Karfin Jumhoriyar Musulinci ta Iran
May 21, 2017 07:33Shugaban Cibiyar Binciken dubaru na Majalisar fayyace maslahar tsarin musulinci na Iran ya ce daga cikin mahiman abubwan da suka sanya kasar Iran ta tsaya da kafafunta shine kasancewar Mutane a fage mababbanta kama daga fagen kare kasa a kallafaffen yaki, aiyukan gina kasa da kuma siyasa
-
Jagoran Juyin Juya Hali Ya Yaba Da Fitowar Mutanen Iran A Zaben Jiya Jumma'a
May 20, 2017 16:00Jagoran juyin juya halin musulunci Aya. Sayyeed Aliyul -Khaminae ya yabawa mutanen kasar Iran kan yadda suka fito konsu da korkotansu don halartar zaben shugaban kasa da sauran zabubbuka na kasar a jiya jumma'a.
-
Sakamakon Farko Na Zaben Shugaban Kasar Iran: Shugaba Hassan ya sami kuri'u miliyan 22,796,468
May 20, 2017 05:03Hukumar Zaben, da ta sanar da sakamakon ta ce; ya zuwa yanzu Shugaba Hassan Rauhani yana kan gaba da kuri'a Miliyan 14.
-
Rahotanni: An Sami Gagarumar Fitowar Al'ummar Iran A Yayin Zaben Shugaban Kasa Na Yau
May 19, 2017 17:54Rahotanni daga suke fitowa daga bangarori daban-daban na kasar Iran musamman a manyan biranen kasar na nuni da cewa miliyoyin al'ummar kasar sun fito don kada kuri'arsu a zaben shugaban kasar da na 'yan majalisun kananan hukumomi da ake gudanarwa a yau din nan Juma'a lamarin da ya sanya aka kara sa'oi kan lokacin da ya kamata a rufe rumfunan zaben.
-
Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci Na Iran Ya Kada Kuri'arsa
May 19, 2017 05:49Da kimanin karfe 8:00 agogon kasar Iran ne jagoran juyin juya halin muslunci a Iran Ayatollah Sayyid Ali Khamenei ya kada kuri'arsa a zaben shugaban kasa da kuma na kananan hukumomi da ake gudanarwa yau a kasar.
-
An Fara Gudanar da Zabukan Shugaban Kasa Da Kananan Hukumomi A Iran
May 19, 2017 05:42An fara gudanar da zabukan shugaban kasa da majalisun kanan hukumomi na Iran, inda miliyoyin jama'a ke ci gaba da shiga cikin layuka a runfunan zabe suna kada kuri'unsu.