Dec 23, 2017 05:23
Babbar sakatariyar kungiyar kasashen renon Ingila (Commonwealth), Patricia Scotland, ta kirayi gwamnatin kasar Kamaru da ta dau matakan ruwan sanyi da kuma tattaunawa wajen magance rikicin da ya kunno kai a yankunan da suke magana da harshen Turancin Ingila na kasar.