Kotun Daukaka Kara Ta Wanke Dan Rahoton RFI
kotun daukaka kara ta sojin Kamaru ta wanke wakilin sashen Hausa na radiyon France International RFI Ahmad Abba daga dukkanin zarge-zargen da ake masa.
Tun a watan Yulin shekarar 2015 ne, jami'an tsaro suka kama Ahmad Abba a yankin Maroua da ke arewacin kasar ta Kamaru lokacin da yake hada wani rahoto da ya shafi kungiyar Boko Haram.
Bayan gurfanar da Ahmad Abba gaban kotu a wancan lokaci aka yanke masa hukuncin daurin shekaru 10 a gidan kan zargin da ake yi masa na halasta kudaden haram da kuma gudanar da ayyukan ta'addanci. To sai dai kuma bayan daukaka kara, a Safiyar jiya Alhamis, Kotun daukaka kara ta Sojin da ke zama a birnin Yaounde ta wanke Ahmad Abba tare da rage hukuncin zuwa daurin watanni 24 a gidan yari.
Hukuncin kotun ya nuna cewa Ahmad Abba wanda ya shafe tsawon watanni 29 a gidan kaso, ya kammala wa'adin da aka yanke masa.