Shugaban Kamaru Ya Gargadi Masu Son Ballewa Daga Kasar
Shugaban kasar kamaru ya ce za su kawo karshen masu son ballewa daga cikin kasar a yankunan da ake amfani da yaren turancin Ingilishi.
Kamfanin dillancin labaran Reuteus ya nakalto shugaban kasar Kamaru Paul Biya na cewa cikin maku guda kacal masu fafutikar ballewa daga kasar sun kashe sojoji 4 da jami'an 'yan sanda 2, domin haka gwamnati za ta kalubalanci wannan lamari saboda yana barazana ga harkokin tsaron kasar.
Paul Biya ya gabatar da wannan jawabi ne a yayin da ya dawo daga taron hadin gwiwa tsakanin kasashen Afirka da Turai game da cin zarafin bakaken fata a kasar Libiya wanda ya gudana a birnin Abidjan na kasar iviry coast.
Daga farkon watan Oktoba zuwa yanzu, rikici tsakanin jami'an tsaron kamaru da masu fafutikar neman ballewa daga kasar na yankin masu amfanin da turanci ingilishi yayi sanadiyar mutuwar fararen hula da dama.abin tuni dai a nan shi ne mafi yawa daga cikin al'ummar kasar ta kamaru na amfani ne da turancin faransanci.
Yadda gwamnatin ta kamaru ke kokarin murkeshe masu amfani da yaran turanci na ingilishin, shi ya sanya wasu dga cikin su suka dauki makamai tare da fafutikar neman balewa daga cikin kasar , inda suka bukaci a gudanar da zaben raba gardama na balewar yankin daga cikin kasar a shekarar 2018.