Najeriya Ta Jaddada Goyon Bayanta Ga Dunkulalliyar Kasar Kamaru
Dec 08, 2017 19:03 UTC
A yau juma'a ne dan sakon musamman na kasar Najeriya zuwa kasar Kamaru Lavan Aba Gashagar ya gana da shugaban kasar Kamaru tare da jaddada masa goyon bayan Najeriya akan fadan da gwamnatinsa ke yi da yan aware.
Jakadan na Najeriya ya kara da cewa; Kasarsa da kuma Kamaru suna da matsaya guda daya akan 'yan awaren yankin da yake magana da harshen Ingilishi,, kuma ta kowace fuska Najeriya ba ta goyon bayan aware.
Yankunan da suke magana da harshen Ingilishi na Kamaru sun tsananta kiraye-kiraye zuwa ga ballewa daga kasar ta Kamaru domin zama kasa mai 'yanci.
Mazauna yankunan masu magana da harshen Ingilishi suna a matsayin kaso 20% na jumillar al'ummar Kamaru mai mutane miliyan 20.
Tags