Pars Today
Rundunar sojin Masar ta kame Sami Anan wani tsohon janar na sojin kasar kan zargin tunzura al'ummar Masar kan sojojin kasar bayan da ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar shugabancin kasar a watan Maris na wannan shekara.
Jami'an tsaron kasar Sudan sun kame shugaban kungiyar Koministe Mukhtar Al-khatib a kokarin ci gaba da kalubalantar masu fafutukar fada da tsadar rayuwa a kasar
Ma'aikatar cikin gida ta kasar Tunisia ta bayyana cewa ya zuwa yanzu ta kama mutane kimani 900 saboda ci gaba da zanga-zangar da suke yi.
Kimanin yarimomi da tsfin hukumomin saudiya 60 ne aka dauke da wurin da ake tsare da su zuwa gidan yari na Alha'ir.
Jami'an tsaron kasar Zimbabwe sun yi awun gaba da wasu ministocin tsohuwar gwamnatin Robert Mugabe su biyu saboda zargin rashawa da cin hanci da kuma amfani da mukaminsu don cimma manufa ta kashin kai.
Babban mai shigar da kara na kasar ta Saudiyya ya ce an kame yarimomin 11 ne bayan da suka yi gangami a bakin fadar mulkin kasar
Ma'aikatar shari'ar garin Borujerd da ke yammacin kasar Iran ta sanar da kame wani dan kasar waje da ya fito daga yammacin Turai a cikin masu kunna wutan rikici a kasar.
Majiyar rundunar sojin Kamaru ta sanar da kame wasu gungun 'yan bindiga a kan iyakar kasar da Equatorial Guinea.
Wani babban lauya a kasar Masar ya bada sanarwan cewa jami'an tsaro a birnin Al-Kahira sun kama wasu daga cikin wadanda suka gudanar da zanga-zangar yin Allahwadai da shugaban kasar Amurka kan abin da ya shafi birnin Qudus.
An kame ministan kudin da tattalin arziki na kasar ta Habasha Almehho Gujo ne bisa zargin cin hanci da rashawa.