Habasha: An Kame Ministan Kudi Da Tattalin Arziki
(last modified Sun, 05 Nov 2017 11:08:47 GMT )
Nov 05, 2017 11:08 UTC
  • Habasha: An Kame Ministan Kudi Da Tattalin Arziki

An kame ministan kudin da tattalin arziki na kasar ta Habasha Almehho Gujo ne bisa zargin cin hanci da rashawa.

Kama ministan ya biyo bayan wani zama da majalisar dokokin kasar ta Habasha ta yi ne inda ta cire masa rigar kariyar da yake da ita.

Gwamnatin kasar ta Habasha ta sanar da kame jami'anta da dama a karkashin shirin fada da cin hanci da rashawa. Kawo ya zuwa yanzu adadin jami'an da aka kama sun kai 40, da suka hada da ministan tattalin arzikin da shugaban kamfanin Sikari da babban jami'i mai kula da ci gaban babban birnin kasar Adis Ababa.

A shekarun 2015/2016 ne dai gwamnatin ta Habasha ta fito da shirin fada da cin hanci da rashawa.