Jan 08, 2019 06:55 UTC
  • An Kama Mutane 816 A Kasar Sudan

Ministan harkokin cikin gida na kasar Sudan ya bayyana cewa tun lokacinda aka fara tashe-tashen hankula na baya-bayan nan kasar Sudan an kama mutane 816.

Kamfanin dillancin Laraban Mehr na kasar Iran ya nakalto ministan cikin gida na kasar ta Sudan Ahmad Bilal Usman yana fadar haka a jiya Litinin. 

Ministan ya kara da cewa mutane 19 ne suka rasa rayukansu tun lokacinda aka fara tashe-tashen hankulan a shekarar da ta gabata.

Amma majiyar kungiyar Amnesty International tana cewa an kashe mutane kimani 40 a rahoton da ta tattara daga kafafe masu amince a kasar ta Sudan.

Tun ranar 19 ga watan Decemban da ta gabata ce mutanen kasar sudan suka fara zanga-zangar yin alllawadai da karin farashin kayakin abinci musamman bredi a kasar. 

Mutanen kasar sudan dai suna bukatar shugaban Umar Hassan Albashir ya kawo karshen shugabancuin kasar da yake yi tun shekara 1993.

A bisa tsarin mulkin kasar Sudan a halin yanzu dai shugaban zai kawo karshen mulkinsa a kasar ne a shekara ta 2020.

 

Tags