An Kama Wasu Tsoffin Ministocin Tsohuwar Gwamnatin Zimbabwe Guda Biyu
(last modified Sun, 07 Jan 2018 11:12:15 GMT )
Jan 07, 2018 11:12 UTC
  • An Kama Wasu Tsoffin Ministocin Tsohuwar Gwamnatin Zimbabwe Guda Biyu

Jami'an tsaron kasar Zimbabwe sun yi awun gaba da wasu ministocin tsohuwar gwamnatin Robert Mugabe su biyu saboda zargin rashawa da cin hanci da kuma amfani da mukaminsu don cimma manufa ta kashin kai.

Kamfanin dillancin labaran Associated Press ya jiyo lauyoyin ministocin biyu wato tsohon ministan harkokin waje Walter Mzembi da ministan makamashi Samuel Undenge suka fadin cewa jami'an tsaron sun kama ministocin biyu da kuma gabatar da su a gaban kotu bisa zargin mummunan amfani da mukami da kuma rashawa da cin hanci.

Ministocin biyu dai sun musanta zargin da ake musu, inda alkalin kotun ya ba da belin su inda ya umurce su da su mika passport dinsu sannan za a ci gaba da sauraren karar a ranar 22 ga watan Janairun nan.

Tun bayan hambare tsohon shugaba Mugabe daga mulkin wannan shi ne karo na biyu da aka gurfanar da ministocinsa a gaban kotu bisa irin wadannan zargi bayan da aka gurfanar da ministan kudi na kasar Ignatius Chombo a gaban kotu a watan Nuwamban da ya gabata.