Pars Today
Wasu gungun 'yan bindigan Libiya sun kaddamar da hari kan rundunar sojin gwamnatin Libiya da ke karkashin jagorancin Janar Khalifah Haftar, inda suka kashe sojojin biyar tare da jikkata wasu na daban.
Wata majiya ta kusa da Halifa Haftar ta ce masu wuce gona da iri ne su ka kai harin a yau lahadi a kudancin harin Darna tare da kashe sojoji biyar.
A yau lahadi ne aka kai hari a gidan da mataimakin shugaban kasar William Ruto ta ke zaune a garin Eldoret da ke yammacin kasar.
Jami'an 'yan sandar Somaliya sun sanar da cewa tashin Bam a babban birnin kasar ya hallaka Mutane 5 tare da jikkata wasu 13 na daban.
Magabatan tsaron kasar mali sun sanar da mutuwar mutane 4 sakamakon harin masu dauke da makamai a gabashin kasar
Kimanin mutane uku ne suka rasa rayukansu yayin da wasu 17 na daban suka jikkata, sanadiyar tashin Bam a arewacin Najeriya.
Wata mota da aka makare da bama-bamai da tarwatse a kusa da wani wajen bincike a garin Arisha da ke arewacin lardin Sina ta Arewa na kasar Masar inda ta lashe rayukan mutane akalla bakwai.
Majiyar tsaro a birnin Bamako ta sanar da gano gawawwakin sojojin kasar a yankunan Gao da Munaka a arewacin kasar ta Mali.
Sojojin kasar Masar Sun sanar da hallaka 'yan ta'adda uku a cibiyar tsibirin Sina
Kamfanin dillancin labarun Associated Press ya ambato majiyar 'yan sanda na cewa harin da aka kai na kunar bakin wake ne, kuma ya ci rayukan mutane 19 da jikkata wasu 23.