Harin Bam Ya Hallaka Mutane Uku A Jihar Bornon Najeriya
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i22592-harin_bam_ya_hallaka_mutane_uku_a_jihar_bornon_najeriya
Kimanin mutane uku ne suka rasa rayukansu yayin da wasu 17 na daban suka jikkata, sanadiyar tashin Bam a arewacin Najeriya.
(last modified 2018-08-22T07:00:27+00:00 )
Jul 26, 2017 01:57 UTC
  • Harin Bam Ya Hallaka Mutane Uku A Jihar Bornon Najeriya

Kimanin mutane uku ne suka rasa rayukansu yayin da wasu 17 na daban suka jikkata, sanadiyar tashin Bam a arewacin Najeriya.

Kamfanin dillancin labaran kasar Faransa ya nakalto wani jami'in hukumar bada agajin gagguawa ta najeriya na cewa wadanda suka harin harin mutane biyu ne, namiji da mace, kuma an kai harin ne a sansanin 'yan gudun hijra na yankin Dalorie kusa da arewacin maiduguri.

A ranar Litinin da ta gabata ma wasu mata sun kai harin kunar baki wake a wani sansanin 'yan gudun hijra na garin maiduguri, lamarin da yayi sanadiyar mutuwar mutane takwas tare da jikkata wasu 15 na daban.

A cikin makunin baya-bayan nan garin maiduguri na fuskantar hare-haren Bam da na kunar bakin wake daga kungiyar ta'addanci nan ta boko haram.

Bira rahoton Majalisar dinkin duniya, daga shekarar 2009 zuwa yanzu, hare-haren ta'addancin da kungiyar boko haram ke kaiwa a Najeriya yayi sanadiyar mutuwar sama da dubu 20 tare da raba wasu kimanin miliyan uku da mahalinsu.