Harin Bam Ya Hallaka Mutane Da Dama A Birnin Magadushu.
Jami'an 'yan sandar Somaliya sun sanar da cewa tashin Bam a babban birnin kasar ya hallaka Mutane 5 tare da jikkata wasu 13 na daban.
Kamfanin dillancin labaran Reuteus ya nakalto jami'an 'yan sandar somaliya a wannan lahadi na cewa, wata mota shake da bama-bamai ta tashi a kusa da wani ofishin 'yan sanda dake birnin Magadushu, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane akalla biyar tare da jikkata wasu 13 na daban.
A cewar majiyar 'yan sandar, an ajiye motar dake shake da bama-bamai ne a wata hanyar mai tsunkoson jama'a da ake kira hanyar Makatul- Mukarrama, kukma mafi yawan mutanen da suka rasa rayukansu a wannan hari ,fararen hula ne.
Duk da cewa har yanzu babu wani gungu ko kungiya da ta dauki alhakin kai harin, to amma dai ana zarkin kungiyar ta'addancin ta Ashabab da kai shi saboda ita ce ta saba kai irin wadannan hare-hare na ta'addanci a cikin kasar.