Mar 02, 2019 12:46 UTC
  • Somalia : Guteres, Ya Yi Tir Da Mummunan Harin Mogadishu

Sakatare Janar na MDD Antonio Guterres, ya yi tir da munanan hare-haren ta'addanci da aka kai Mogadishu, babban birnin Somalia.

Cikin wata sanarwa da kakakinsa Stephane Dujjaric ya fitar, Antonio Guterres ya jadadda goyon bayan MDD ga al'umma da gwamnatin kasar Somalia yayin da suke kokarin cimma zaman lafiya.

A kalla mutane ashirin ne suka rasa rayukansu kana wasu sama da 100 suka raunana, sanadiyyar harin da aka kai cikin wata mota a kusa da wani otel dake birnin Mogadishu, ranar Alhamis da dare.

Bayan harin, maharan sun kuma  yi garkuwa da mutane har na tsawan sa'o'i 22.

Tuni dai kungiyar Al-Shabab mai alaka da Al-Qaeda ta dauki alhakin kai harin, tana mai cewa otel din ta kai wa hari, wanda ya yi fice tsakanin 'yan siyasa da jami'an gwamnati da kuma attajirai.

A halin da ake ciki dai gwamnatin Somalia, ta bukaci 'yan kasar dasu dafa mata a yakin da take da kungiyar ta A'shebab mai tsatsauran ra'ayin addini.

Tags