Libya: An Kashe Sojojin Gwamnati Biyar A Gabacin Kasar.
Jul 30, 2017 19:09 UTC
Wata majiya ta kusa da Halifa Haftar ta ce masu wuce gona da iri ne su ka kai harin a yau lahadi a kudancin harin Darna tare da kashe sojoji biyar.
Bugu da kari majiyar ta shaida wa kamfanin dillancin labarun Faransa cewa baya ga wadanda aka kashe, wasu sojojin hudu sun jikkata.
Dakarun Halifa Haftar dai suna fada da kungiyoyi masu wuce gona da iri da su ke a gabacin kasar, tare da kokarin kwace iko da garin Darnah da nan ne cibiyar al-ka'idah a cikin kasar.
Tun bayan kifar da gwamnatin Khaddafi a 2011 da sojojin Nato su ka yi, kasar Libya ta fada cikin rashin tsaro.
Tags