Feb 24, 2017 04:50
Laifin yaki na daga cikin muhimman laifuffukan da aka yi bayanin ma'anarsa a fili ciki takardu da dokokin kotunan kasa da kasa. Sashi na 8 na dokokin hukunta laifuffukan na kasa da kasa yayi bayanin abubuwan da suke tabbatar da laifin yaki, wanda daga cikinsu akwai kisan gilla, azabtarwa mai tsanani, cutar da jikin mutum, kai hari da gangan kan fararen hula, ruwan bama-bamai kan gidajen mutane ko gine-ginen da ba na soji ba da kuma amfani da makamai masu guba da iskar gas mai makure mutum.